Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Sauyin yanayi zai sa 'yan Afrika fiye da miliyan 100 a matsanancin talauci- MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan yadda dumamar yanayi ke barazana ga mutane fiye da miliyan 100 wadanda ke cikin matsanancin talauci a Afrika sakamakon yiwuwar zagwanyewar tsaunukan dusar kankarar da nahiyar ke da su cikin shekaru 20 masu zuwa.

Dumamar yanayi na barazana ga nahiyar Afrika fiye da ko'ina a Duniya.
Dumamar yanayi na barazana ga nahiyar Afrika fiye da ko'ina a Duniya. SEYLLOU AFP/File
Talla

Cikin rahoton wanda Majalisar ta fitar gabanin babban taron yanayi na COP26 da zai gudana a Glasgow ta sake bayyana irin kalubalen da ke tunkaro nahiyar ta Afrika sakamakon dumamar yanayi da zai zama kari kan kamfar abinci da matsanancin talauci da al’ummar yanki ke fuskanta dai dai lokacin da ake samun karuwar jama’a.

Rahoton ya ce nan da shekarar 2030 akwai kiyasin mutum miliyan 118 da ke halin matsanancin talauci a nahiyar ta Afrika su fara fuskantar fari da ambaliyar baya ga matsanancin yanayin zafi matukar ba a dauki matakan da suka kamata a yaki da matsalar ba.

Shugabar sashen kula da tattalin arzikin yankunan karkara na tarayyar Afrika Josefa Leonel Correia Sacko ta ce akwai bukatar daukar matakan yaki da dumamar yanayi don ceto miliyoyin matalautan da ke rayuwa a nahiyar ta Afrika.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya gwada misali da wani makamancin da hukumar kula da yanayi ta Duniya ta fitar da ke cewa mutanen da ibtila’in zai shafa na rayuwa ne kasa da dalar Amurka biyu a kowacce rana.

Sacko ta bayyana cewa matsalolin dumamar yanayi zai shafi hatta tattalin arzikin kasashen yamma da saharar Afrika wadanda za sus amu koma baya da kasha 3 cikin dari a ma’aunin GDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.