Isa ga babban shafi
Najeriya-Bauchi

Yadda sauyin yanayi ke haddasa ambaliyar ruwa a sassan Najeriya

Sauyin yanayi na ci gada da haifar da ambaliyar tare da sanya asarar rayuka da dukiyoyi a sassan Najeriya. Karamar Hukumar Kirfi, mai tazarar kilomita 60 daga garin Bauchi ta fuskanci mummunar matsalar ambaliyar da ta haddasa rushewar gidaje fiye da dubu 2 da gonaki fiye da dubu 5, ambaliyar da yankin ke ganin irinta ta farko cikin shekaru 70. Wakilinmu a Bauchi Ibrahim Malam Goje, ya ziyarci karamar hukumar domin ganewa idan sa lamarin, kuma ga rahotan da ya hada mana.

Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a Najeriya.
Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a Najeriya. AP - Michael Probst
Talla

Tun kafin wannan gagarumin iftila’in, kwararru sun yi ta fadakar da jama’a kan matakan kariya daga wannan matsala.

Malam Nasiru Cheledi da Baba Lawan Cheledi suna daga cikin daruruwan jama’ar da ambaliyar ta raba da matsugunansu.

“An yi hasarar gine ginen kwana da kuma dan abinda ba a rasa ban a dabbobi zuwa ban-daki – ban-daki haka amma dai dakunan kwana sune dai manyan abubuwan da aka fi rasawa akai”.

“Eh kamar dai shi yadda wannan abu ya kasance ya faru ne ta sanadiyyar kwararowar ruwa daga daji  ya zo ya shiga gidaje mun yi iya kokarinmu don tarewa abu ya gagara. Shiga gidajen nan da zai yi tun ana samun kamar iya guiwa ya kai ga kugu, ya shiga dakuna ya lalata kayan dake ciki”.

Kasancewar an dauki lokaci mai tsawo yankin na Kirfi bait aba fuskantar irin wannan matsala ba, wasu mutanen yankin sun bige da gine gine ko yin noma akan hanyoyin ruwa, lamarin da kwararru ke dangantawa da matsalar. Dr Abubakar Suleman, malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi, ya yi bayani kan abin da kan jawo ambaliya.

“Hanyoyin ruwa wadansu mutane z aka ga suna gine gine, hanyoyin ruwa wadanda aka tanada saboda idan ruwa ya zo ya wuce, mutane saboda rashin hankali idan sun debo shara ta bola daga gidajensu, basa da wurin zubarwa sai cikin wadannan ramuka yau da gobe kuma sai ka ga sun cika”.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad ya kai ziyayar jaje garin na Kirfi inda ya tabbatar wa al’ummar yankin kudurin gwamnati na daukar matakin magance wannan matsala.

“Za mu dauki matakai iri iri na ilimi da hikima mu ga ina ne ruwan ke fitowa kuma ina za a masa hanya sannan wadanda suka zauna kan hanyar ruwa, za mu ba su shawara su tashi.”

A halin da ake ciki, mamakon ruwan da aka tashi da shi yau a garin na Kirfi, ya sake mayar da hannun agogo baya inda wasu karin gidaje da a baya basu rushe ba, suka rushe.

Ibrahim Malam Goje, Bauchi, RFI Hausa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.