Isa ga babban shafi
Sudan

Ambaliyar ruwa ta tagayyara mutane fiye da dubu 10 a Sudan

Ambaliyar ruwa ta rushe dubban gidaje tare da mamaye tituna da dama a Sudan, sakamakon saukar ruwan saman kamar da bakin kwarya a Khartoum, babban birnin kasar.

Hoton da ke nuna illar illar da ambaliyar ruwa tayi a sassan Sudan.
Hoton da ke nuna illar illar da ambaliyar ruwa tayi a sassan Sudan. www.unocha.org
Talla

Zalika a Atbara, birnin da ke arewa maso gabashin kasar ta Sudan, kamfanin dillancin labarai na SUNA ya ruwaito cewa ruwan saman mai karfi yayi sanadin rushewar gidaje da dama.

A ranar Alhamis da ta gabata hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ta ce kimanin mutane dubu 12 da ke jihohi 8 daga cikin 18 iftila’in ya shafa a kasar.

A shekarar bara mamakon ruwan sama ya tilastawa gwamnatin Sudan ayyana dokar ta baci ta tsawon watanni uku, sakamakon tagayyara mutane akalla dubu 650 da ambaliyar ruwa ta yi, tare da lalata gidaje sama da dubu 110.

An dai saba samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a Sudan daga watan Yuni zuwa Oktoba a kowace shekara, inda ake samun hasarar rayuka da dimbin dukiya ciki har da amfanin gona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.