Isa ga babban shafi
Duniya - Ambaliyar Ruwa

Karin mutane miliyan 86 sun shiga hatsarin fuskantar ambaliyar ruwa

Wani rahoton kwararru kan muhali da matsalar sauyin yanayi ya ce adadin mutanen da ambaliyar ruwa ke shafa da kuma wadanda ke cikin hatsarin fuskantar iftila’in a duniya ya karu zuwa kusan kashi 25 cikin 100, a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Mutane suna jiran ceto a saman rufin motoci yayin da suke makale a kan hanyar da kogin Kinugawa ya cika, wanda guguwar Etau ta haddasa a Joso, lardin Ibaraki da ke kasar Japan. An dauki wannan hoton a 10 Satumba, 2015.
Mutane suna jiran ceto a saman rufin motoci yayin da suke makale a kan hanyar da kogin Kinugawa ya cika, wanda guguwar Etau ta haddasa a Joso, lardin Ibaraki da ke kasar Japan. An dauki wannan hoton a 10 Satumba, 2015. REUTERS/Kyodo
Talla

Masanan da suka wallafa wannan rahoto sun ce sun tattara hujjojinsu ne daga bayanan tauraron dan adam da ke nuna samun karin mutane miliyan 86 da a yanzu haka ke zaune a cikin yankuna masu fama da ambaliyar ruwa a sassan duniya.

A halin da ake ciki iftila’in ambaliyar ruwa ke kan gaba tsakanin sauran masifu masu alaka da yanayi wajen addabar muhalli, sakamakon karuwar yawan ruwan sama dake sauka, lamarin da kwararru suka alakanta kai tsaye da matsalar Sauyin Yanayi.

Mummunan ambaliyar ruwa, ta tafka barna a kasashen Indiya, China, Jamus da Belgium.
Mummunan ambaliyar ruwa, ta tafka barna a kasashen Indiya, China, Jamus da Belgium. DIBYANGSHU SARKAR AFP/File

Manyan misalan yadda ambaliyar ruwa ta tagayyara jama’a a baya bayan nan sun hada da abinda ya auku a kasashen Indiya, China, Belgium da kuma Jamus, inda ambaliyar ta lakume rayukan mutane da dama, gami da lalata dukiya mai tarin yawa, mafi akasari a yankunan da marasa karfi ke zaune.

A mafi rinjayen lokuta taswirar da masana ke samarwa kan ambaliyar ruwa na dogaro ne da nauyin ruwan saman da ke sauka da kuma tumbatsar teku da koguna wajen tattara bayanai kan ambaliyar ruwa, sai dai galibi suna gaza samun bayanan kan yankunan da a tarihi ba sa fuskantar iftila’in.

Yadda garin Erftstadt, a gundumar Cologne, ya cika da ambaliya bayan ruwan sama mai ƙarfi, 16 ga Yuli, 2021.
Yadda garin Erftstadt, a gundumar Cologne, ya cika da ambaliya bayan ruwan sama mai ƙarfi, 16 ga Yuli, 2021. AFP - HANDOUT

Don cike gibin ne gungun masu bincike na Amurka suka rika bibiyar bayanan tauraron dan adam na hotuna sau biyu a rana dangane da bala’o’in ambaliyar ruwa fiye da 900 da suka auku a kasashe 169 tun daga 2000.

Kawo yanzu Jumilar murabba'in kilomita miliyan 2 da dubu 230 ambaliyar ruwa ta shafa a sassan duniya tsakanin shekarar 2000 zuwa 2018, alamarin da ya rutsa da akalla mutane miliyan 290.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.