Ambaliyar Ruwan Sama ta kashe mutane 150 a Afghanistan
Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu, a yayinda wasu kuma 150 suka bace, sakamakon ambaliyar ruwan saman da ta shafi Arewacin kasar Afghanistan haka kuma arewa maso gabashin Kabul, babban birnin kasar.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka dai, ana ci gaba da gudanar da aikin ceton jama’a, domin samun damar ceto masu sauran numfashi bayan saukar ruwan sama babu kakkautawa dake dauke da iska mai karfin gaske da ya mamaye gundumar Kamdesh da ke lardin Nuristan mai tazarar kilomita 200 arewa maso gabashin Kabul.
Bayanai da hukumomin kasar suka bayar sun nuna cewa mutane dari da hamsin ne suka bata , a yayinda sama da gidajen zaman jama’a 80 suka rushe sakamakon mummunar ambaliyar ruwan saman da ya mamaye yankin.
A cewar mai Magana da yawun gwamnan Nuristan, wato saeed Momand, kawo yanzu sama da mutane 60 ambaliyar ruwa ta kashe a yankin.
A ko wace shekara dai saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya na yin sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a kasar ta Afghanistan.
Yanzu hada dai ana cike da fargabar cewa gidajen zaman jama’a da dama ne, galibi daga yankunan karkara ke kan rushewa sakamakon rashin ingancin da suke da shi.
A bara dai mutane da dama ne suka rasa rayukansu a sanadiyar ambaliyar da ta biyo bayan saukar ruwan da ya mamaye yankunan lardin Parwan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu