Isa ga babban shafi
China - Ambaliya

Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutane 25 a China

Akalla mutane 25 ne suka rasa rayukan su a wata ambaliyar ruwa da ta faru a kasar China, lamarin da ya raba mutane sama da dubu 2 da muhallan su. Inda wasu hotuna da fayafayan bidiyo da aka rika yada su a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya kaiwa mutane har wuya saboda yawansa tare da ruguza gidaje.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane da dama a wasu yankunan kasar China, 20 ga watan Yuli 2021.
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane da dama a wasu yankunan kasar China, 20 ga watan Yuli 2021. STR AFP
Talla

Ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon ruwan sama kaman da bakin kwarya da aka rika shekawa, wanda ya sanya madatsun ruwa da manyan koguna suka rika ambaliya.

Tuni dai shugaban kasar Xi Jingping ya bayyana ambaliyar a matsayin mummunan tashin hankalin da ya faru a kasar, yana mai cewa dole a dauki matakin gaggawa duk kuwa da cewa lamarin na neman gagarar hukumomin bada agajin gaggawa na kasar.

Munin ambaliyar ya tilastawa jami’an sojoji da na ‘yan sanda shiga cikin aikin ceto, la’akari da yadda ambaliyar ta shafi sama da mutane miliyan 10.

Rahotanni sun bayyana cewa rabon da a sami ruwan sama mai karfi da yawan na bana a China tun shekaru 60 da suka gabata.

Babban abin fargabar a yanzu shine yadda hukumomi a kasar suka bayyana cewa akwai yiwuwar a sami ruwan saman da ya fi na yanzu yawa da karfi nan ba da jimawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.