Isa ga babban shafi
Jamus - Ambaliyar Ruwa

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta halaka a Turai ya zarce 180

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta lalata a kasar don duba irin barnar da ta yi, da kuma ganawa da wadanda suka tsira bayan an kwashe kwanaki ana ruwan sama mai karfin gaske a yammacin Turai, wanda yayi sanadin mutuwar mutane akalla 183 yayin da wasu da dama suka bace.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Gwamnan Jihar Rhineland-Palatinate Malu Dreyer yayin da suka ziyarci ƙauyen Schuld da ambaliyar ruwa ta lalata kusa da Bad Neuenahr-Ahrweiler, Rhineland-Palatinate, Jamus 18 ga Yuli, 2021.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Gwamnan Jihar Rhineland-Palatinate Malu Dreyer yayin da suka ziyarci ƙauyen Schuld da ambaliyar ruwa ta lalata kusa da Bad Neuenahr-Ahrweiler, Rhineland-Palatinate, Jamus 18 ga Yuli, 2021. REUTERS - POOL
Talla

Merkel ta yi tattaki zuwa ƙauyen Schuld da ke jihar Rhineland-Palatinate, daya daga cikin yankunan da suka fi tagayyara a yammacin Jamus inda kogin Ahr ya share gidaje tarea da barin tarkace mai yawa kan tituna bayan tumbatsar da ya yi.

AShugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firayim Ministan Jihar Rhineland-Palatinate Malu Dreyer yayin da suka ziyarci ƙauyen Schuld da ambaliyar ruwa ta lalata kusa da Bad Neuenahr-Ahrweiler, Rhineland-Palatinate.
AShugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firayim Ministan Jihar Rhineland-Palatinate Malu Dreyer yayin da suka ziyarci ƙauyen Schuld da ambaliyar ruwa ta lalata kusa da Bad Neuenahr-Ahrweiler, Rhineland-Palatinate. REUTERS - POOL

Jami’an ceto sun ce akalla mutane 156 ne suka mutu tun daga ranar Laraba dalilin ambaliyar ruwa mafi muni da aka gani a kasar Jamus.

A jihar Rhineland-Palatinate kadai, mutane 110  suka mutu yayin da wasu 670 da suka jikkata.

A Belgium kuwa, mutane akalla 27 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.