Isa ga babban shafi
China

Ambaliya ta kashe Mutane sama da 200 a China

Ruwan sama da aka tafka a China ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 200 tare da tursasawa dubbai kauracewa gidajensu. Rahotanni sun ce kusan mutane 200 suka bata a lardin Hebei bayan ruwan saman ya haifar da ambaliya da zabtarewar kasa.

Ambaliyar ruwa ta shafi wani yanki na Beijing
Ambaliyar ruwa ta shafi wani yanki na Beijing REUTERS
Talla

Ambaliyar ta shafi sassan biranen China yayin da gidaje sama da 50,000 suka rushe.

Hukumomin China sun ce Sama da mutanen kasar miliyan takwas da rabi ambaliyar ta shafa.

Mutanen yankin da bala’in ya shafa sun soki hukumomin da rashin sanar da su ko yin gargadi ga aukuwar al’amarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.