Isa ga babban shafi
Canjin yanayi

Coca-Cola da Pepsi sun fi gurbata muhalli a Duniya - Bincike

Wani rahoton kwararru ya bayyana kamfanin lemun kwalba na Coca-Cola a matsayin wanda ya fi gurbata muhalli a duniya, inda takwaransa na Pepsi ke biye da shi.

Yadda rubobi ke haifar da gurbatar Muhalli.
Yadda rubobi ke haifar da gurbatar Muhalli. Luis ACOSTA AFP/File
Talla

Rahoto ya gano cewa, robobin da wadannan kamfanoni ke zuba lemunsu a ciki, sun karade sassa da dama na duniya  a matsayin shara.

A yayin tattara alkaluman binciken, sama da mutane dubu 11 suka sadaukar da kansu a kasashen duniya 45 wajen aikin tsaftace gabar tekuna tare da kwashe tarin sharar robobin da wadannan kamfanoni ke samarwa,

Wasu bayanai na cewa, an tattara sharar robobi sama da dubu 330 bayan an  yi amfani da su sau daya tal kuma robobin Cocoa-Cola ke kan gaba, sannan na PepsiCo da ke biye da shi, yayin da robobin Unilever ke a matsayi na uku.

A karo na hudu kenan a jere da Coca-cola ke kasancewa kan gaba a jerin kamfanonin da robobinsu ke gurbata muhalli, amma a karon farko kenan da Unilever ya haura mataki na uku.

Wannan rahoton da aka fitar na zuwa ne mako guda gabanin fara babban taron sauyin yanayi na COP26 a birnin Glascow, inda kasashen duniya za su sake nazartar hanyoyin magamce matsalar ta sauyin yanayi da ke barazana ga halittun duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.