Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Gurbacewar iskar gas ta yi munin da ba a taba gani ba

Gabanin taron sauyin yanayi na COP26 a kan ta’azarar dumamar yanayi, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, gurbatacciyar iskar gas a sararin samaniya  ta kai kololuwar da ba ta taba kaiwa ba a shekarar da ta gabata.

Yadda iskar gas ke gurbata sararin samaniuya.
Yadda iskar gas ke gurbata sararin samaniuya. AP - Sam McNeil
Talla

Hukumar Kula da Yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce gurbatacciyar iskar da ke taruwa a sararin samaniya na iya haifar da yanayi mara armashi tare da fadada munanan tasirinta a kan muhalli da tattalin arziki.

Hukumar ta ce, tsaiko da aka samu a fannonin ayyukan habaka tattalin arziki sakamakon bullar annobar Covid 19 ya rage gurbatacciyar iskar da masana’antu ke fitarwa, sai dai an gaza fahimtar tasirin haka a yadda iskar ke taruwa a sararin samaniya.

Mujallar da hukumar ke wallafawa a game da sauyin yanayi ta ruwaito cewa, gurbatacciyar iskar da aka samu a shekarar da ta gabata ta zarta yadda aka saba samu daga tsakanin shekarun 2011 da 2020, kuma hakan ya ci gaba a shekarar 2021.

Duba da rashin saurin gushewar iskar Carbon Dioxide, yanayin zafin da ake fuskanta a halin yanzu zai ci gaba tsawon gwamman shekaru, ko da kuwa an rage fitar da gurbatacciyar iskar kacokan.

Za a  gudanar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniyar ne daga ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 12 ga Nuwamba a birnin Glasgow na kasar Scotland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.