Isa ga babban shafi
Canjin yanayi

MDD ta bukaci samar da ninki 10 na tallafin rage tasirin sauyin yanayi

Majalisar dinkin duniya ta ce kasashe masu tasowa na bukatar ninki 10 na kudaden da aka ware don kare kansu daga mummunan tasirin sauyin yanayi dake ci gaba da tsananta.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. AP - EDUARDO MUNOZ
Talla

A yayin da taron sauyin yanayi na 26 ke fafutukar rage hayaki mai gurbata yanayi, tare da tabbatar da cewa an takaita zafin yanayin a kan digiri 1 da rabi a ma’aunin Celsius kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar Paris, sabon rahoton hukumar kula da muhalli ta majalisar dinkin duniya ya jaddada bukatar a yi wa kasashe damara a kan tasirin sauyin yanayi.

Ganin yadda guguwa, ambaliya da fari suka ta’azzara sakamakon dumamar yanayi, kasashe matalauta sun yi kira ga masu kumbar susa a taron yanayi na COP26 da su mutunta alkawarin da suka yi na samar da dala biliyan 100 duk shekara don tunkarar matsalar ta dumamar yanayi.

Rahoton hukumar kare muhallin ta majalisar dinkin duniya, ya gano cewa kasashe masu tasowa kawai za su bukaci kashin abin da ya tasamma dala biliyan 300 a cikin shekara guda zuwa shekarar 2030, da biliyan 500 zuwa 2050 wajen daukar wadannan matakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.