Gurbata muhallin duniya zai ta'azzara a bana - Rahoto
Wani sabon rahoto da aka wallafa a yau Alhamis ya bayyana cewa, yawan fitar da iska mai gurbata muhalli zai ta’azzara a cikin wannan shekara ta 2021 zuwa matakin da aka gani gabanin bullar cutar Korona.
Wallafawa ranar:
Rahoton wanda aka wallafa a yayin da kusan kasashen duniya 200 ke gudanar da taron sauyin yanayi a birnin Glasgow ya ce, fitar da iska mai gurbata muhalli a bana za ta kai irin matakin da aka gani a shekara ta 2019, sabanin bara, lokacin da aka samu sassauci saboda takaita hada-hada a sanadiyar cutar Korona.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, rage fitar da hayaki mai lalata muhalli zuwa kashi 1.5 a ma’aunin Celcius kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar birnin Paris, zai takaita yawan mace-mace da barna a yanzu.
Amma a cewar Majalisar Dinkin Duniyar, sai an rage fitar da irin wanann mugun hayakin da kashi da akalla rabi kafin cimma burin rage mace-macen nan da shekara ta 2030.
Sannan sai an daina ma fitar da hayakin baki daya kafin rage mace-macen nan da shekara ta 2050 kamar yadda masana kimiyar ta Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.
Farfesar Sauyin yanayi a Jami’ar East Anglia ta Birtaniya, Corrine Le Quere ta ce, wannan sabon rahoton gaskiya da gaskiya ne, domin kuwa ya nuna ainihin abin da ke wakana a sassan duniya a daidai lokacin da shugabannin kasashe suka hallara a birnin Glasgow don samar da mafita daga matsalar ta sauyin yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu