Isa ga babban shafi
Rasha-Turkiya

Shugabannin Rasha da Turkiya sun kauracewa taron Paris kan Libya

Shugabannin kasashen Turkiya da Rasha sun kauracewa taron zaman lafiyar Libya da shugaba Emmanuel ke jagoranci yau juma’a a birnin Paris, taron da ya samu halartar shugabannin kasashe da dama.

Wakilcin wasu kasashe da ke halartar taron Paris don tattaunawa kan zaman lafiyar Libya.
Wakilcin wasu kasashe da ke halartar taron Paris don tattaunawa kan zaman lafiyar Libya. REUTERS - POOL
Talla

Rahotanni sun ce duk da matakin aikewa kasashen biyu gayyata zuwa taron don tattaunawa kan batun janye dakarun kasashen duniya daga cikin kasar mai fama da rikicin shekaru 10, kasashen biyu sun aike da kananun wakilai ne kadai don halartar taron.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da bisa al’ada ba a fiya ganinsa a taron kasashen yammacin Turai ba, shi ke wakilartar Moscow a wannan taro yayinda Turkiya ta aike da mataimakin ministan wajenta Sedat Onal.

Kusan kasashe 30 yanzu haka ke halartar taron a Paris don tattaunawa kan yadda zaman lafiya zai dawo Libya gabanin zaben kasar na watan Disamba.

Sojin hayar kamfanin Wagner na Rasha da hadin gwiwar dakarun LNA da ke gabashin Libyae da Sojin hadaddiyar daular larabawa da na Masar na cikin wadanda ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a kasar.

A bangare guda Turkiya na matsayin babbar mashawarciyar tsohuwar gwamnatin Libyan yayinda ta ke taimaka mata ta fuskar tsaro da hadin gwiwar mayakan Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.