Isa ga babban shafi
Libya-Zabe

Kusa mutum miliyan 3 sun yi rijistar zaben watan Disamba a Libya

Hukumar zabe a Libya ta kulle shafin yanar gizon da ta bude don baiwa al’ummar kasar damar yin rijistar zabe da nufin tunkarar zaben watan Disamba, ko da ya ke har yanzu akwai shakku kan yiwuwar gudanar da zaben kamar yadda aka tsara duk da tsagaitawar rikicin kasar tsawon watanni.

Jagoran gwamnatin rikon kwarya a Libya Abdel Hamid Dbeibah.
Jagoran gwamnatin rikon kwarya a Libya Abdel Hamid Dbeibah. © Mahmud Turkia, AFP
Talla

Hukumar ta bakin kakakinta Imad al-Sayed ta ce al’ummar kasar miliyan 2 da dubu dari 8 da 30 ne suka yi rijistar ta Intanet yayinda aka bude dama ga ‘yan kasar da ke ketare su faro tasu rijistar daga yau laraba.

Kasar ta Libya mai yawan mutane miliyan 7 na shirin tunkarar babban zabe ne a kokarin kawo karshen yakin basasar da ta fada tun bayan hambarar da gwamnatin Moamer Kadhafi a shekarar 2011

Tun cikin watan Oktoban bara ne aka cimma yarejejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarori biyu masu rikici da juna a kasar bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya kai ga dorawa gwamnatin rikon kwarya alhakin gudanar da zabe a ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa.

Sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba game da shirye-shiryen zaben wanda ya ragewa kasa da watanni 4 a gudanar bayan da wakilan da Majalisar Dinkin Duniya ta zaba su 75 don sanya idanu kan kamun ludayin siyasar kasar suka gaza amince da tanade-tanaden zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.