Isa ga babban shafi
Libya-Ghaddafi

Dan Ghaddafi ya bayyana aniyar takarar shugaban Libya

Saif al-Islam, dan shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi  da aka kashe a shekarar 2011 ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar, tare da maido da hadin kanta, bayan yakin da aka shafe shekaru 10 ana yi ya wargaza ta.

Saif al-Islam Ghaddafi, dan shugaban Libya  Marigayi Muammar Ghaddafi.
Saif al-Islam Ghaddafi, dan shugaban Libya Marigayi Muammar Ghaddafi. © Ammar El-Darwish, AP
Talla

Ya bayyana haka ne  wata ganawa da ya yi da jaridar ‘New York Times’ a gidansa da ke garin Zintan, yammacin kasar da ke arewacin Afrika.

Dan shekaru 49 din, wanda kafin shekarar 2011 ake mai kallon wanda zai gaji mahaifinsa ya ce a cikin shekaru 10 da suka wuce, babu abin da ‘yan siyasa suka tsinana wa kasar face ukuba da tashin hankali, yana mai cewa lokaci ya yi da za a  koma yadda ake a da.

An shafe shekaru  ba tare da an san inda al-Islam, wanda kotun hukunta laifukan yaki ke nema ruwa jallo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.