Isa ga babban shafi
Faransa-Libya

An gurfanar da kamfanonin da suka taimaka wa Gaddafi na Libya

Masu shigar da kara sun tuhumi shugabannin wasu kamfanonin Faransa da ake zargi da taimaka wa tsohon shugaban Libya Moammar Ghaddafi wajen yi wa wasu masu adawa da shi leken asiri kafin daga bisani ya kama su tare da azabtar da su.

Marigayi tsohon shugaban Libya Moammar Kadhafi
Marigayi tsohon shugaban Libya Moammar Kadhafi Reuters/Huseyin Dogan
Talla

Kungiyar  Kare Hakkin Bil’adama ta FIDH ta ce, a makon jiya ne, aka tuhumi tsohon shugaban kamfanin Amesys, Philippe Vannier a birnin Paris dangane da zargin sa da hadin baki wajen azabtar da masu hamayya da marigayi Ghaddafi.

Kazalika an tuhumi shugaban kamfanin fasaha na Nexa, Olivier Bohbot da wasu karin jagorori  biyu na kamfanin da hadin baki wajen azabtarwa tare da tilasta wa ‘yan adawar bacewa.

An zargi kamfanonin biyu da sayar da kyamarorin leken asiri ga Libya da Masar wadanda aka yi amfani da su wajen murkushe masu adawa da gwamnatin marigayi Ghaddafi.

Sanarwar da Kungiyar  FIDH ta fitar ta ce, wannan abun da kamfanonin suka aikata na a matsayin manyan laifuka da za a iya tuhumar su a kai.

Tuni Kungiyar Kare Hakkin Bil’adaman ta shigar  da kara, inda kuma aka bude  bincike  kan zarge-zargen da ake yi musu bayan Mujallar Wall Street ta fara fallasa rahoton leken asirin a 2011, lokacin da jama’a suka gudanar da jerin zanga-zangar adawa da gwamnatoci a kasashen Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.