Isa ga babban shafi
Libya-Kadhafi

Ana cika shekaru 10 da kisan shugaba Moamer Kadhafi na Libya

Yau ake cika shekaru 10 da kisan tsohon shugaban kasar Libya Moamer Kadhafi biyo bayan juyin-juya halin kasar da ya juye zuwa rikici tare da yin awon gaba da kujerar mulkinsa. Rikicin na Libya da ya samu goyon bayan manyan kasashen duniya da kungiyar tsaro ta NATO, masana na ganin shi ya assasa tashe-tashen hankula da ma bazuwar makamai a nahiyar Afrika.

Tsohon shugaban kasar Libya, Moammar Kadhafi.
Tsohon shugaban kasar Libya, Moammar Kadhafi. © RFI
Talla

Moamer Kadhafi wanda ya mulki Libya da takalmin karfe har tsawon shekaru 42 tun daga 1969 bayan karbe mulki daga tsarin sarakunan gargajiya da kasar ke kai a baya, gabanin shekarar ta 2011 da kasashen duniya suka yiwa gwamnatinsa taron dangi, kisansa ya gaza taimakawa wajen tabbatar da Demokradiyya, batun da ke matsayin farfagandar da aka yi amfani da ita wajen samun goyon bayan 'yan kasar a hambarar da mulkin nasa.

Shekara guda yanzu haka da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a kasar amma masana na ganin abu ne mai wuya hatta zaben da ake shirin gudanarwa ya iya warware rikicin da Libyan ke ciki.

A ranar 20 ga watan Oktoban shekarar ta 2011 ne wasu tsagerun ‘yan tawaye suka bi sahun shugaba Kadhafi har zuwa mahaifarsa Sirte tare da kashe shi a tsakar titi baya ga jan ganganar jikinsa a tsakar kasuwa.

Har zuwa yanzu Libya ta gaza murmurowa daga illar da hambarar da gwamnatin Kadhafi ta haifar mat aba kadai ta bangaren tsaro ba har da tattalin arziki da kuma tsanantar rayuwa sabanin sassaukar rayuwa da kasar ke yi a baya.

Wani masani a cibiyar bincike ta Verisk Maplecroft, Hamis Kinnear ya ce kasar ta Libya ta fi kasancewa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali gabanin juyin-juya halin idan aka kwatanta da halin da ta ke ciki a yanzu.

Tun bayan hambarar da gwamnatin ta Kadhafi matsalolin ‘yan bindiga dadi da masu safarar mutane dama karuwar kwararar baki zuwa turai baya ga barayin man fetur sun ta’azzara a kasar ta arewacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.