Isa ga babban shafi

Kasashen duniya za su dafawa Libya wajen shirya zaben kasar na watan disemba

Gwamnatin rikon kwaryar kasar Libya na karbar bakunci wakilan kasashen duniya da ke halartar wani taro kan yadda za a samar da hadin kai tsakanin ‘yan kasar gabanin babban zaben da ake shirin gudanarwa a cikin watan disamba mai zuwa.

Taron sassanta yan siyasa na kasar Libya
Taron sassanta yan siyasa na kasar Libya © MOHAMMED EL SHAIKHY/AFP
Talla

Majalisar Dimkin Duniya da kuma gwamnatin hada-ka ta Libya, na kokarin ganin cewa an samu goyon bayan illahirin bangarorin siyasa na kasar don ganin cewa an shirya zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar ranar 24 ga watan disamba na wannan shekara ta 2021.

Birnin Benghazi na kasar Libya
Birnin Benghazi na kasar Libya Abdullah DOMA AFP/File

Wasu daga cikin kasashen Duniya sun soma nuna goyan baya ga tsarin sake dawowwa da mulkin farrar fula kusan shekaru goma da mutuwar Ghadafi a kasar ta Libya.

 

Wasu daga cikin dakarun kasashen waje dake aiki da rundunar kasar Libya
Wasu daga cikin dakarun kasashen waje dake aiki da rundunar kasar Libya AP - Hazem Ahmed

A watan yuni shekarar bana ne Faransa ta sake bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli na kasar Libya, bayan da aka rufe shi shekaru 7 da suka gabata saboda tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan boren da aka yi wa gwamnatin Kanar Kaddafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.