Kotu ta daure Shugaban babban bankin kasar Iran
A Iran ,kotun kasar ta zartas da hukuncin dauri ga wani tsohon Shugaban babban bankin kasar da aka sama da laifin wawashe akalla milyan 160 na dalla da ta janyo asarar kusan kudadden shiga ga asusun gwamnatin kasar na milyan 20 na kudi Euros.
Wallafawa ranar:
Tsohon jami’in bankin kasar mai suna Valiollah Seif da ya jagoranci babban bankin kasar kama daga shekara ta 2013 zuwa 2018 ya na mai shekaru69 zai fuskanci dauri na shekaru 10 duk da cewa ya na da ikon daukaka kara a hukumance.
Wasu daga cikin mukaranban sa da kotu ta zartasawa da hukunci yanzu haka sun hada da mataimakin sa wanda zai share shekaru takwas a daure sai wani mai taimakawa mataikamakin Shugaban bankin da aka sama da laifin cin hantsi tareda karbar kudadden kasashen waje ta barauniyar hanya.
Wannan dai ne karo na farko da daya daga cikin shugabanin babban bankin kasar ya fuskanci shara’a dangane da batuttuwan da suka shafi cin hantsi da rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu