Isa ga babban shafi
Iran-Saudiya

Tattaunawa kan sulhunta rikicin Iran da Saudiyya ta kankama

Kasar Iran ta ce ana samun gagarumar ci gaba a tattaunawar da su ke da Saudi Arabia domin ganin sun dinke barakar da ke tsakanin su ta bangaren diflomasiya.

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi.
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi. © Présidence iranienne, AFP
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh ya ce an samu gagarumar ci gaba a bangaren tsaron Yankin Tekun Fasha, a tattaunawar da aka fara lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Hassan Rouhani.

Kasashen Iran da Saudiya basa ga maciji da juna a tsakanin su, rikicin da yayi matukar illa wajen zaman lafiyar Yankin Tekun Fasha da kuma rarraba kawunan kasashen larabawa.

Saudiya c eke jagorancin Musulmi mabiya Sunnah a duniya, yayin da Iran ke jagoranci mabiya Shi’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.