Isa ga babban shafi
IRAN-FARANSA

Tsohon shugaban Iran Banisadr ya rasu yau a Paris

Shugaban kasar Iran na farko tun bayan juyin juya halin shekarar 1979 Abolhassan Banisadr ya rasu yau a wani asibitin birnin Paris, inda yake gudun hijira, yana da shekaru 88 a duniya.

Tsohon shugaban Iran Abolhasan Banisadr
Tsohon shugaban Iran Abolhasan Banisadr Jerome DELAY AFP/Archivos
Talla

Majiya daga iyalan sa ta shaidawa  kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar bayan daukar dogon lokaci yana jinya, Banisadr ya rasu yau asabar a asibitin  Salpetriere dake kudu maso gabashin Paris.

Iyalan tsohon shugaban sun tabbatar da rasuwar shi a sanawar da suka gabatar inda suka bayyana tsohon shugaban a matsayin mai kare ‘yancin jama’a.

Sanarwar tace, suna shaidawa mutanen Iran da masu gwagwarmayar ‘yanci cewar tsohon shugaban ya rasu bayan ya dauki dogon lokaci yana fama da rashin lafiya.

Abolhassan Banisadr lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar 7 ga watan Mayun shekarar 1991 dangane da littafin da ya wallafa
Abolhassan Banisadr lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar 7 ga watan Mayun shekarar 1991 dangane da littafin da ya wallafa AFP - ALI REZA MASHALKOUBEH

Sai dai ma’aikatar shari’ar Iran ta bayyana Banisadr a matsayin wanda ya dauki dogon lokaci yana yiwa kasar illa da kuma bata mata suna a karkashin Faransa da kasashen Yammacin duniya.

Banisadr ya lashe zaben shugaban kasar Iran na farko a shekarar 1980 abinda ya bashi damar jagorancin ta bayan juyin juya halin Islamar da aka yi a kasar, kafin kawar da gwamnatin sa majalisar dokoki tayi a shekarar 1981 sakamakon tabarbarewar dangantaka tsakanin sa da shugaban addinin kasar Ayatollah Ruhollah Khomeini.

Tun daga wancan lokaci ne Banisadr ya koma Faransa inda yake gudun hijira.

An dai haife shi a ranar 22 ga watan Maris na shekarar 1933 a kauyen Hamadan dake Yammacin Iran, kuma an bayyana shi a matsayin mai goyan bayan ‘yancin addini.

Daga cikin mukaman da ya rike harda da ministan tattalin arziki da kuma ministan harkokin waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.