Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

A shirye muke mu farfado da yarjejeniyar nukiliyarmu - Iran

Iran ta ce za ta tattauna da manyan kasashen duniya da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyarta a farkon watan Nuwamba.

Cibiyar Sarrafa Nukiliyar Iran
Cibiyar Sarrafa Nukiliyar Iran AP
Talla

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran  Saeed Khatibzadeh ya bayyana hakan, yana mai cewa idan aka yi niyya, ba batu ba ne da ke daukar lokaci mai tsawo kamar yadda  ya  dauki gwamnatin Biden.

Khatibzadeh ya ce, gwamnatin Shugaba Ebrahim Raisi da ke da kasa da kwanaki 55 da darewa karagar mulki, ba ta tunanin shirya tattauanawar za ta dauke ta sama da kwanaki 90, yana mai cewa, Iran za ta shirya ganawar a tsakiyar watan Nuwamba mai zuwa.

Wannan shi ne karon farko da Iran ta sanya lokaci don yiwuwar komawa kan teburin tattaunawa.

Yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 ta dan saukaka wa Iran  takunkumai saboda matsin lamba kan shirinta na nukiliya, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke sa ido.

Shugaban Amurka na wancan lokacin Donald Trump ya janye kasar daga yarjejeniyar da ta kunshi bangarori daban-daban, sannan ya fara saka wa kasar takunkumi a shekarar 2018, abin da ya sa ta sake dawo da shirinta na nukiliyar sannu a hankali tun daga shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.