Isa ga babban shafi
Iran-Kwallon Kafa

'Yan matan Iran za su fara halartar filin wasa

A karon farko cikin shekaru biyu, mata a Iran za su halarci filin wasan kwallon kafa da ke birnin Tehran domin nuna goyon bayansu ga tawagar kasar wadda za ta kara da Koriya ta Kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Matan Iran a filin wasa na Azadi mai yawan kujeru dubu 80
Matan Iran a filin wasa na Azadi mai yawan kujeru dubu 80 ATTA KENARE AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan mahukuntan kasar sun bai wa matan izinin halartar filin wasan na Azadi a ranar 12 ga watan Oktoban nan domin kallon wasan kai tsaye.

Raban da matan Iran su halarci filin wasan tun cikin watan Oktoban 2019, lokacin da Iran din ta lallasa Cambodia da kwallaye 14-0.

Kafin wannan lokaci, hukumomin Iran sun haramta wa mata shiga filin wasan a shekara ta 1979 domin kare mutuncinsu da kuma hana su cakuduwa da maza.

Amma Hukumar Kwallon Kafa ta Duniuya ta yi wa Iran matsin lamba don ganin ta janye dokar hana su shiga filin wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.