Isa ga babban shafi
Duniya - Canjin Yanayi

Shugabannin Kiristoci sun shiga gangamin yaki da matsalar sauyin yanayi

Shugabannin addinin Kirista na majami'un Katolika, na gargajiya da aka fi sani da Orthodox a turance da kuma na Anglican sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan neman gaggauta aiwatar da matakan kawo karshen matsalar sauyin yanayi.

Shugabannin addinin Kirista na majami'un Katolika, na gargajiya da aka fi sani da Orthodox a turance da kuma na Anglican, Fafaroma Francis, Patriarch Bartholomew na 1 da kuma Archbishop na Canterbury, Justin Welby.
Shugabannin addinin Kirista na majami'un Katolika, na gargajiya da aka fi sani da Orthodox a turance da kuma na Anglican, Fafaroma Francis, Patriarch Bartholomew na 1 da kuma Archbishop na Canterbury, Justin Welby. © Franco Origlia / Getty Images
Talla

Fafaroma Francis, Patriarch Bartholomew na 1, da kuma Archbishop na Canterbury, Justin Welby ne, suka fitar da sanarwar, da ke jan hankalin duniya kan sauraro da kuma kiyaye gragadin da kwararru ke yi kan halin da Muhalli ko Yanayin Duniya ke ciki na gurbacewa.

Karo na farko kenan da shugabannin bangarorin manyan mujami’un na Addinin Kirista ke irin wannan kira kan makomar duniya dangane da batun dumamar yanayi, gabannin taron da majalisar dinkin duniya za ta jagoranta a kasar Scotland kan matsalar sauyin yanayin a watan Nuwamban da ke tafe.

Taron duniyar kan Sauyin Yanayi wanda Fafaroma Francis ke fatan halarta, zai gudana a birnin Glasgow ne daga 31 ga Oktoba zuwa 12 ga Nuwamba.

Sai dai kasashe da dama, musamman matalauta wadanda aka barsu a baya kan shrin allurar rigakafin Korona sun bayyana damuwa kan yiwuwar ba za su samu halartar babban taron kan Sauyin Yanayi ba saboda cutar.

Tuni dai gammayar kungiyoyin masu rajin kare muhalli na kasa da kasa fiye da dubu 1 da 500 suka bukaci dage taron da ke tafe a Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.