Dumamar yanayi na sauya wa tsuntsaye fasalin halittarsu
Wani sabon rahoton masana na nuna cewa, matsalar dumamar yanayi da ake fama da ita a duniya, na shafar hatta dabbobin da ke rayuwa a sararin samaniya, inda matsalar ke sauya musu zubin halitta.
Wallafawa ranar:
Rahoton masanan na cewa, fasalin jikin tsuntsaye kamar akukuturu na Australia da zomaye na Turai na sauyawa saboda tasirin matsalar dumamar yanayi.
Sara Ryding mai bincike a Jamiar Deakin ta kasar Australia wadda ta jagoranci binciken dabbobin, na ganin lokaci ya yi da za a bai wa dabbobi kulawa domin su tafi daidai da zamani.
Wannan binciken da aka wallafa a wannan Talatar, ya yi nazarin wasu nazarce-nazarce na baya game da sauyin halittun dabbobi a dalilin sauyin yanayi a duniya, inda aka fara gano sauyin a cikin tsuntsaye.
Binciken ya karas da cewa, ana samun kari wajen girman aku na kasar Australia da kashi 4 cikin 100 bisa yadda yake a shekara ta 1871.
Haka ma an gano cewa, sauran tsuntsaye na wasu kasashen Turai sun kara girman jiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu