Isa ga babban shafi
Taliban-MDD

Guterres ya roki kasashe su tattauna da Taliban saboda Al'ummar Afghanistan

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya roki kasashen duniya da ci gaba da tattaunawa da kungiyar Taliban domin kare al’ummar Afghanistan daga tagayyara. Kiran na Guterres na zuwa ne a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke fuskantar barazanar rushewa saboda katse tallafin da ake bata.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. Javier Soriano AFP/Archivos
Talla

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya yi wannan kira ne a lokacin wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, inda ya bayyana fargaba karuwar karfin masu tsattsauran ra’ayi a yankin Sahel, saboda nasarar da kungiyar Taliban ta samu na sake komawa kan mulkin Afganistan.

Guterres ya ce babban aikin da ke gaba duniya yanzu haka a Afghanistan shi ne tallafawa al’ummar kasar wadanda miliyoyi daga cikinsu ke fuskantar hatsarin yunwa, dan haka ya zama dole a dauki matakan hana rugujewar tattalin arzikin su.

Sakataren ya kara da cewar babu tabbas dangane da sakamakon shiga tattaunawa da gwamnatin Taliban to amma ganawar ta zama dole ne idan har ana son hana Afghanistan zama cibiyar ta'addanci da kuma take ‘yancin da mata suka samu a shekarun baya.

A lokacin da aka tambaye shi game da hatsarin maimaituwar abin da ya faru a Afghanistan a Sahel, babban magatakardan na majalisar dinkin duniya bayyana fargaba kan tabbatuwar hasashen, tare da kafa hujjar fara kutsen da masu tssattsauran ra’ayi suka yi a Mozambique, Ivory Coast da kuma Ghana, bayan tashin hankalin da ya addabi sassan Mali, Burkina da Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.