Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Manyan nade-naden Taliban ya kunshi shugabanninta masu hadari

Sabbin nade-naden kungiyar Taliban a Afghanistan ya ta’allaka kan manyan-manyan shugabanninta da ke dauke da takunkuman kasashen Duniya da na Majalisar Dinkin Duniya dai dai lokacin da zanga-zangar adawa da jagorancin kungiyar ke ci gaba da tsananta a sassan kasar.

Ma'assasin kungiyar Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar tare da wasu jigan-jigan shugabannin kungiyar.
Ma'assasin kungiyar Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar tare da wasu jigan-jigan shugabannin kungiyar. AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

A yayin da Taliban din ke cikin hidimar kafa gwamnati, da nufin rikidewa daga kungiyar masu tayar da kayar baya zuwa masu mulki, jami’an tsaron sun yi ta kokarin dakile jerin zanga-zangar adawa da sabbin masu madafun iko da ke ci gaba da fuskanta a sassan kasar, wadda ta kai ga kisan mutane 2 a birnin Herat da ke yammacin Afghanistan.

Mullah Mohammad Hassan Akhund, wani babban minista a zamanin da Taliban ta yi mulki da takalmin karfe a cikin shekarun 1990, shi ne kungiyar ta nada a matsayin Firaminista.

Taliban dai ta alkawarta cewa za ta kafa gwamnati ta wajen la’akari da bambamce bambamcen da ke tsakanin al’ummar kasar, amma sai ga shi ilahirin manyan makaman sabuwar gwamnatin  sun shiga hannun manyan shugabanninta, da kuma ‘yayan kungiyar Haqqani, sashen Taliban mafi hadari da aka fi sanin su da aiwatar da munanan hare hare.

Sai dai an jiyo kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid ya na cewa, za a dama da al’ummar sauran sassan kasar, inda ya jaddada cewa sabuwar gwamnatin ta wucin gadi ce gabanin samar da wata a nan gaba.

Jim kadan bayan sanar da sabuwar gwamnatin, sai Hibbatullah Akhundzada, shugaban kungiyar na boye, wanda ba a taba ganinsa a bainar jama’a ba, ya fitar da wata sanarwar da ke cewa sabuwar gwamnatin za ta yi aiki tukuru wajen jaddada shari’ar Musulunci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.