Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Taliban ta yi shelar mallake Afghanistan baki daya

Taliban ta yi shelar nasarar kammala kwace ilahirin yankunan Afghanistan da suka hada da lardin Panjshir, yanki na karshe da ke kalubalantar sabuwar gwamnatin kungiyar.

Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid
Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Bayan kwashe kwanaki mayakan na Taliban na fatattakar dakarun da suka kudiri aniyar bai wa lardin na Panjshir kariya daga mulkin kungiyar ne, a yau litinin Taliban ta sanar da kwace iko da yankin wanda ke nufin ilahirin sassan kasar yanzu haka na karkashin ikonta.

Tun tsakiyar watan Agustan da ya gabta, Taliban ta kwace mulkin kasar bayan gazawar sojin Afghanistan da kuma tserewar shugaba Ashraf Ghani da ma ficewar dakarun sojin Amurka, lamarin da ya kawo karshen yakin shekaru 20 da kasar ta gani.

A wani taron manema labarai da Taliban ta kira yau Litinin, kakakinta Zabihullahi Mujahid, ya ce Taliban ta yi nasarar murkushe barazanar da take fuskanta daga yankin na Panjshir, yayin da ya yi gargadi kan duk wani yunkuri na kalubalantar mulkinsu, a bangare guda kuma ya umarci tsaffin mambobin kungiyar da su koma bakin aiki a Panjshir.

A cewar Mujahid bayan nasararsu ta kammala kwace Panjshir, Afghanistan ta kammala ficewa daga kangin yaki.

Haka zalika Taliban ta kuma yi gargadi da kakkausar murya kan duk wani yunkurin tsirarun kungiyoyin ta’addanci da ke kokarin kawo tarnaki ga harkokin tafiyar da mulki a Afghanistan, inda ta ce cikin sauri za su murkushe kowacce barazana.   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.