Isa ga babban shafi
Taliban-Pakistan

Taliban ta tarwatsa zanga-zangar mata masu kin jinin Pakistan

Mayakan Taliban sun tarwatsa dandazon matan da ke zanga-zangar kin jinin Pakistan a birnin Kabul na Afghanistan inda mayakan suka rika harbi a iska wanda ya kai ga tarwatsa taron matan wadanda suka taru a yankuna daban-daban na birnin.

Dandazon matan da ke zanga zangar kin jinin Pakistan a Afghanistan.
Dandazon matan da ke zanga zangar kin jinin Pakistan a Afghanistan. Hoshang Hashimi AFP
Talla

Zanga-zangar wadda ta kankama yau Talata, na matsayin babban kalubale ga Taliban wadda ta kwace iko da Afghanistan a watan jiya, dai dai lokacin da tsoro ke ci gaba da samun wajen zama a zuciyoyin al’ummar kasar dangane da mulkin na Taliban wadda kawo yanzu ba ta sanar da kafa gwamnati ba.

Akalla mabanbantan zanga-zanga 3 mata suka jagoranta a birnin na Kabul yau talata inda su ke kalubalantar salon mulkin Taliban na shekarun 1996 zuwa 2001 lokacin da kungiyar ta rika zartas da hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifi yayinda aka rika yanke hannun barayi.

Guda cikin masu zanga-zangar wadanda suka yi dandazo a farfajiyar ofishin jakadancin Pakistan da ke Kabul wadda ta bayyana sunanta da Sarah Fahim ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa matan Afghanistan sun gaji da yaki, suna bukatar a gina musu kasarsu suna bukatar zaman lafiya tare da cikakken ‘yanci.

Masu zanga-zangar sun zargi Pakistan da kitsa yadda lamurra ke tafiya a kasar musamman bayan ziyarar shugaban sashen leken asirin kasar Faiz Hameed a Kabul cikin karshen mako.

Pakistan ita ce kasa ta farko cikin kasashe 3 da zuwa yanzu suka amince da mulkin Taliban kuma ita ce kasa daya tilo da tun a baya ake zargi da mara baya ga kungiyar haka zalika ita ke bata mafaka a lokuta da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.