Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Taliban ta fara nuna karfin makamanta a Afghanistan

A ci gaba da bukukuwan nuna farinciki da suke yi game da kwace Iko da Afghnaistan, ‘yan Taliban sun fara nuna irin karfin makaman da suke da su da kuma wandanda suka gada da suke kallo a matsayin ganimar yaki.

Wasu sojojin Taliban a filin jirgin sama na birnin Kabul
Wasu sojojin Taliban a filin jirgin sama na birnin Kabul WAKIL KOHSAR AFP
Talla

Tun bayan da dakarun Amurka suka karkare ficewa daga kasar Afrghanistan, mayakan na Taliban ke ci gaba da bukukuwa ta hanyar nuna karfin makaman da suke da su da kuma wadanda dakarun Amurka suka bari a kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, mayakan sun jera manyan tankunan yaki a hanyar zuwa garin Kandahar, inda ta daddaura musu tutocin kasar ta Afghanistan.

An hango manyan-manyan bindigogi na dakarun Amurka  da sauran makamai rataye a wuyan dakarun Taliban da aka jera su.

Baya ga wannan kuma, manyan motocin daukar kaya na ta shawagi cikin manyan garuruwa cike da manya-manyan makamai da bindigogi da ake yiwa lakabi da masu jigida.

Akwai kuma jiragen yaki masu saukar ungulu da su ma ke ta shawagi a filin jirgin saman birnin Kabul duk kuwa da yadda ake ganin mayakan ba su da kwararrun matuka jirgin sama.

A ganin masharhanta, mayakan na Taliban na nuna kayan yakin nasu ne don bayyana wa duniya cewa, a shirye suke da su tunkari rikon gwamnatin kasar tare da gargadi ga duk kasar da ke shirin kai musu wargi da ta kiyayi kanta a fakaice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.