Isa ga babban shafi
Afghanistan

Majalisar Dinkin Duniya zata shirya taron tara kudin taimakawa 'yan Afghanistan

Babban magatarkadar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai yi tattaki zuwa Geneva don kiran babban taro kasa da kasa kan taimakawa kasar Afghanistan a ranar 13 ga watan Satumba.

Majalisar Dinkin Duniya zata shirya taron tarawa 'yan kasar Afghnistan kudi saboda bukatun agajin gaggawa bayan da Taliban ta kwace iko.
Majalisar Dinkin Duniya zata shirya taron tarawa 'yan kasar Afghnistan kudi saboda bukatun agajin gaggawa bayan da Taliban ta kwace iko. Aamir QURESHI AFP
Talla

Kakakinsa Stephen Dujarric ya bayyana haka cikin wata sanarwa, yana mai cewa Kasar Afghanistan da yanzu haka ke karkashin ikon 'yan Taliban bayan shefe shekaru 20 na gwabza yaki, na fuskantar "gagarumin bala’in jinkai.

"Taron zai ba da shawarar wajen hanzarta samar da kudade don ayyukan ceton rayuka; da yin kira don samun cikakkiyar agajin jin kai don tabbatar da cewa 'yan Afghanistan sun ci gaba da samun muhimman bukatun yau da kullum.

Ya kuma ce dole ne a kiyaye nasarorin ci gaba a cikin ƙasar kuma haƙƙin mata wani muhimmin abu ne na zaman lafiyar Afghanistan nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.