Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Kwamitin tsaron MDD zai yi zama na musamman kan Afghanistan

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na musamman a wannan Litinin domin tattauna bukatar da  Faransa da  Birtaniya suka gabatar game da yiyuwar samar da kudurin da zai ayyana yankin tsaro a matsayin tudun mun tsira a Afghanistan don bayar da damar ci gaba da kwashe mutane daga birnin Kabul.

Mayakan Taliban a mashigin filin tashi da saukar jiragen saman Kabul dake kasar Afghanistan 28/08/21.
Mayakan Taliban a mashigin filin tashi da saukar jiragen saman Kabul dake kasar Afghanistan 28/08/21. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da lamurran tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a birnin Kabul, domin ko a wannan Litinin makamai masu linzami sun fada a wasu unguwanni da ke birnin.

Yunkurin na kasashen Faransa da Birntaniya na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke shirin kawo karshen aikin kwashe mutanen ta daga kasar ta Afghanistan daga gobe talata 31 ga watan Agusta.

Lura da cewa mafi yawan kasashen duniya sun ce ko bayan janyewar Amurka za su ci gaba da kokarin kwashe fararen hula daga filin sauka da tashin jiragen saman birnin Kabul, wannan ya sa Faransa da Birtaniya a matsayinsu na mambobi Kwamitin Sulhu suka bijiro da wannan shawara don samar da kariya matuka don ci gaba da wannan aiki bayan janyewar Amurka.

To sai dai manazarta na ganin cewa shata yankin tsaro a birnin na Kabul kawai ba zai wadatar ba sai tare da samun goyon bayan ‘yan Taliban da ke matsayin sabbin magabatan kasar Afghanistan ta Afghanistan.

A jiya lahadi Kungiyar Taliban ta tabbatar wa kasashen duniya akalla 100 ciki har da Amurka, Birtaniya, Faransa da kuma Jamus damar ci gaba da kwashe mutanensu daga kasar matukar da sai sun mallaki takardun da ke ba su damar yin balaguro zuwa ketare.

Sai dai shugaban Faransa Emmanuel Macron na cewa matakin na Taliban ba wai yana nufin cewa kasashen duniya sun amince da kungiyar ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.