Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Faransa da Birtaniya na bukatar samar da tudun mun tsira a Afganistan

Faransa da Burtaniya za su bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta yi kokarin samar da "wani yanki a matsayin tudu" a Kabul babban birnin Afghanistan inda za’a gudanar da ayyukan jin kai.

Tổng thống Pháp Emmanuel Macron tiễn khách - thủ tướng Anh Boris Johnson (T), sau buổi ăn trưa ở điện Élysée, ngày 22/08/2019.
Tổng thống Pháp Emmanuel Macron tiễn khách - thủ tướng Anh Boris Johnson (T), sau buổi ăn trưa ở điện Élysée, ngày 22/08/2019. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya bayyana wannan bukata yayin hira da jaridar Journal du Dimancehe yace matakin na da matukar muhimmanci, wadda zai samar da tsarin hatta ga Majalisar Dinkin Duniya don yin aiki cikin gaggawa.

Bugu da kari, shugaba Macron yace samarda yanki mai aminci, zai ba da dama ga kasashen duniya "su ci gaba da matsa lamba kan 'yan Taliban," wadanda yanzu ke kan karagar mulki a Afghanistan.

Mambobin dindindin na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya  da suka hada da Faransa, Burtaniya, Amurka, Rasha da China - za su hadu ranar Litinin don tattauna halin da ake ciki a Afghanistan.

Paris da London za su yi amfani da damar gabatar da daftarin ƙuduri wanda "ke da nufin ayyana, ƙarƙashin ikon Majalisar Dinkin Duniya, 'yanki mai aminci' a Kabul, wanda zai ba da damar ci gaba da ayyukan jin kai", in ji Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.