Isa ga babban shafi
Afghanistan

Kasashen duniya sun fara maida martani kan harin bama-bamai a Afghanistan

Kasashen duniya sun fara mayar da martani game da tagwayen bama-baman da suka tashi a filin jirgin saman Kabul wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 95 cikin su har da sojojin Amurka 13.

Sojan Faransa a filin tashi da saukar giragen saman Kaboul dake Afghanistan, 24/08/21.
Sojan Faransa a filin tashi da saukar giragen saman Kaboul dake Afghanistan, 24/08/21. AP
Talla

Amurka

Da take mayar da martani kasar Amurka ta bakin shugaban ta Joe Biden, ya ce babu makawa sai Amurka ta gano wadanda ke da hannu wajen tayar da wannan Bam da ya hallaka sojojin kasar, wanda shine mafi munin hari da ya rutsa da sojojin Amurka tun shekarar 2011.

Suma dai mayakan Taliban ba’a bar su a baya ba, wajen Tur da wannan hari, sai dai sun zargi Amurka da sakaci kasancewar harin ya faru ne a wajen da har yanzu ke karkashin ikon ta.

Rasha

A nata Bangaren kasar Russia ta ce abin takaici ne yadda Amurka ta sanya mutane fita tare da tururuwa a filin jirgin saman Kabul wanda shine ya baiwa mayakan IS damar kai wannan mummunan hari, tana mai cewa harin tsanstsar rashin imani ne.

China

China ma dai na cikin kasashen da suka mayar da Martanin, inda ta ce ta kadu matuka da jin Labarin harin, kuma wannan na nuna cewa har yanzu yanayin tsaro a Afghanistan na cikin mummunan hali.

Birtaniya

Prime Minista Boris Johnson na Burtaniya cewa ya yi harin abin takaici ne, kuma yana mika sakon ta’aziyyar sa ga dukannin iayalan wadanda harin ya rutsa da su, a madadin dukkanin al’ummar Burtaniya.

Sauran kasashe irin su Canada da Hukumar Lafiya ta duniya da kungiyar kasashe musulmi, sai kuma kasashen Gabas ta tsakiya da na kudancin Amurka sai kungiyar kasashen Africa duk sun yi Allah wadai da harin.

IS

Tuni dai kungiyar IS ta fito fili ta ce magoya bayanta ne suka kai wannan hari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 95 ciki har da sojojin Amurka 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.