Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Taliban za ta bari a ci gaba da kwashe jama'ar Afghanistan

Jamus ta ce, ta samu tabbaci daga wakilin  Taliban cewa, za a bai wa ‘yan Afghanistan masu halastattun takardu  damar ficewa daga kasar koda kuwa bayan cikar wa’adin ranar 31 na janyewar Amurka daga kasar.

Dimbin mutane ne ke dakon ficewa daga birnin Kabul na Afghanistan
Dimbin mutane ne ke dakon ficewa daga birnin Kabul na Afghanistan AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Manzan Musamman na kasar Jamus Markuz Potzel ya fadi a shafinsa na Twitter cewa, ya gana da wakilin Taliban Sher Mohd. Abbas Stanikzai, wanda ya tabbatar masa cewa, ‘yan Afghanistan masu halastatun takardu za su ci gaba da ficewa daga kasar koda kuwa bayan karewar wa’adin ranar 31 ga watan Agustan nan da aka kayyade tun da farko.

Gwamnatin Jamus dai ta bayyana cewa, sojojin kasashe mambobin NATO da ke taimakawa wajen gudanar da aikin kwashe jama’ar Afghanistan da ke cikin hatsari, ba za su iya ci gaba da aikinsu ba muddin Amurka ta janye.

Gwamnatin  Jamus ta ce, tana son tabbatar da cewa, mutanen Afghanistan masu rauni da suka hada da ‘yan rajin kare hakkin bil’adama da tsoffin ma’aikatan da suka yi wa hukumomin  Jamus hidima, sun samu hanyar ficewa cikin salama daga  kasar bayan cikar wa’adin.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maas ya ce, gwamnatin Belin za ta nemi  kwashe mutane daga kasar koda kuwa bayan cikar wa’adin.

A nata bangaren , shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce, dole ne kasashen  duniya su yi zaman tattaunawa da Taliban muddin suna son tabbatar da zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.