Amurka ta murkushe wani sabon hari kan filin jiragen saman Kabul
Sojojin Amurka sun kaddamar da harin sama a Kabul a inda suka nufi wani da ake zargin dan kunar bakin wake ne da ke da niyyar kai hari filin jirgin saman, kamar yadda jami’an Amurka suka sanar.
Wallafawa ranar:
Jami'an, wadanda suka nemi a sakaya sunansu, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kai harin ne kan 'yan kungiyar IS-K, dake adawa da dakarun kasashen Yamma da kuma Taliban, kuma ita ce ke da alhakin kai harin kunar bakin wake a wajen filin jirgin sama a ranar Alhamis.
Harin na IS-K, reshen kungiyar Islamic State (IS), ya kashe a kalla 'yan Afghanistan 90 da sojojin Amurka 13 yayin da ake ci gaba da aikin kwashe mutane bayan kwace Kabul a ranar 15 ga watan Agusta.
Wannan na zuwa ne bayan da Amurka ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake kai wani harin ta’addanci makamancin wanda aka kai a filin jirgin saman Kabul.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu