Isa ga babban shafi
Afghanistan

Amurka ta kai hari da kurman jirgi kan mabuyar IS a Afghanistan

Rundunar sojin Amurka ta ce wani hari ta sama da ta kai ya kashe wani ƙusa a ƙungiyar IS da ta kai harin kunar bakin wake a filin jirgin saman Kabul da ke kasar Afghanistan ranar Alhamis, wanda ya kasha sama da mutane 95 ciki har da sojojin Amurka 13.

Jirgin yakin Amurka maras matuki
Jirgin yakin Amurka maras matuki © dr
Talla

Rundunar ta ce harin da ta kai ta sama da jirgi maras matuki a gundumar Nangahar, ya kashe mutumin da Amurka ta ce shi ke kitsa wa ƙungiyar IS yadda za ta kai hare hare.

Hakan na zuwa ne adai-dai lokacin da ake cikin rudani a filin jiragen saman Kaboul, inda har yanzu masu neman neman tserewa suka cika makil inda aka shiga matakin karshe, yayin da ake gargadin sake kai harin ta'addanci.

Wannan mataki ya tilasta aikin tare tsakanin dakarun Amurka da mayakan Taliban wajen aikin kula da kwashe mutane daga filin tashi da sukar jiragen saman birnin Kaboul dake Afghanistan, saboda fargabar sabon hari daga IS bayan harin kunar bakin wake da ya hallaka mutane 95 ciki harda sojojin Amurka 13.

Tuni reshen kuingiyar dake yankin ya yi ikirarin kai harin, yayin da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da kai harin da jirgi mara matuki kan "wadanda ta kira wadanda suka tsara harin" daga kungiyar masu da'awar jihadi a gabashin Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.