Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Taliban ta nada sabbin manyan jami'an gwamnatin Afghanistan

Kungiyar Taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan, wata guda bayan kwace iko da kasar dai dai lokacin shugabancinta ke fuskantar tarnaki musamman daga dandazon matan da ke ci gaba da zanga-zangar neman ‘yanci da kuma shigar da su harkokin tafiyar da gwamnati.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid yayin taron manema labarai na yau talata da ke sanar da nadin mukarraban tafiyar da gwamnatin kungiyar.
Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid yayin taron manema labarai na yau talata da ke sanar da nadin mukarraban tafiyar da gwamnatin kungiyar. AP - Rahmat Gul
Talla

A wani taron manema labarai da kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid ya gabatar yau talata, ya sanar da cewa dukkanin mukaman da za a nada yanzu za su kasance na rikon kwarya inda ya bayyana Mullah Mohammad Hasan Akhund a matsayin shugaban sabuwar gwamnatin yayinda guda cikin ma’assasan kungiyar ta Taliban Abdul Ghani Baradar zai zama mataimaki.

Haka zalika Mujahid ya sanar da sunan Mullah Yaqub, dan marigayi Mullah Omar tsohon shugaban majalisar koli kuma guda cikin wadanda suka kafa kungiyar a matsayin ministan tsaro sai kuma Sirajuddin Haqqani a matsayin ministan cikin gida wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban kungiyar ta Taliban.

Haka zalika nade-naden na Taliban ya sanar da sunan Amir Khan Muttaqi babban mai shiga Tsakani na kungiyar a Doha matsayin ministan harkokin waje.

A cewar Mujahid Taliban za ta yi kokarin shigar da wasu mutane daga waje cikin kowanne sashe na kasar don basu mabanbantan mukamai.

Tun cikin watan Agustan da ya gabata aka tsammaci kungiyar ta sanar da kafa sabuwar gwamnatin wadda tun a wancan lokaci ta sha alwashin shigar da kowanne bangare har da kananun kabilu cikin tafiyar ko da ya ke babu tabbacin tafiya ta yiwu tare da mata saboda dokoki da ka’idoji da kungiyar ke kai wadanda suka haramtawa mata shiga harkokin tafiyar da gwamnati.

Taliban dai na da manya-manyan kalubale a gabanta musamman a al’amuran da suka shafi karancin kudin tafiyar da gwamnati da kuma tsananin bukatar agajin da yankuna da dama ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.