Isa ga babban shafi
Taliban

Taliban ta bukaci daliban jami'a mata da su rika sanya nikabi

Kungiyar Taliban ta bukaci dalibai matan dake zuwa jami’oin kasar masu zaman kan su a Afghanistan da su dinga sanya nikabi suna rufe fuskokin su, kuma ya zama wajibi a raba azuzuwa tsakanin maza da mata.

Wasu mata da suka gudanar da zanga -zangar neman hakkokinsu a kasar Afghanistan karkashin jagorancin Taliban. 3/09/21.
Wasu mata da suka gudanar da zanga -zangar neman hakkokinsu a kasar Afghanistan karkashin jagorancin Taliban. 3/09/21. AP - Wali Sabawoon
Talla

Wata takardar umurnin da hukumomin ilimin Taliban suka gabatar, tace malamai mata ne kawai zasu koyar da dalibai mata, idan kuma babu malamai mata, toh sai dai tsofaffi maza da aka tabbatar suna da halayen kirki.

Sanarwar tace dokar ta kuma shafi jami’oi da manyan kwaleji masu zaman kan su wadanda suka sauya manufofin su bayan kifar da gwamnatin Taliban a shekarar 2001.

A wancan lokacin an hana ‘yam mata da mata samun ilimi a makarantu saboda dokar hana su zama aji guda da maza da kuma bukatar samar musu da ‘dan rakiya daga cikin ‘yan uwan su kafin su bar gida kamar yadda doka ta tanada.

Sabuwar dokar dai bata kunshi rufe daukacin fuskokin mat aba, sai dai rufe wasu sassa, amma banda idanun su.

A shekarun da suka gabata, an daina amfani da hijabin dake rufe daukacin fuskar mata a birnin Kabul bayan kawar da gwamnatin Taliban da akayi, sai dai wasu garuruwa da kauyukan kasar.

Wannan sabuwar dokar na zuwa ne a daidai da ake shirin bude makarantu domin fara karatu wannan litinin din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.