Isa ga babban shafi
Afghanistan

An sake bude filin jragen saman Kabul bayan karkare jigilar ceton mutane

Kamfanin jiragen sama na Ariana da ke Afganistan ya sanar da ci gaba da jigilar fasinjoji tsakanin Kabul da da wasu manyan biranen larduna uku na kasar a yau Asabar, bayan da wata tawagar kwararru daga Qatar ta sake bude filin jirgin saman domin sufurin cikin gida da kuma karbar kayayyakin agaji daga ketare.

Filin jiragen saman Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.
Filin jiragen saman Kabul, babban birnin kasar Afghanistan. Aamir QURESHI AFP
Talla

Jigilar jiragen saman kamfanin na Ariana na gudana ne a tsakanin Kabul, birnin Herat da ke yammacin Afghanistan, Mazar-i Sharif a arewaci da kuma Kandahar a kudancin kasar.

Sake bude filin jiragen saman na Kabul ya kasance muhimmin mataki ga ‘yan Taliban, a yayin da suke neman daidaita lamurra a birnin da ma kasar baki daya, bayan gagarumar nasarar da suka samu a ranar 15 ga watan Agusta, na kawar da gwamnatin Ashraf Ghani.

An rufe filin jirgin sama na Kabul tun bayan kawo karshen aikin kwashe dubban mutane daga Afghanistan da Amurka ta jagoranta domin tseretar da su daga mulkin Taliban da suke tsoron kasancewa a karkashinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.