Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mayakan Taliban sun tarwatsa zanga-zangar mata a Kabul

Mayakan Taliban sun yi harbi cikin Iska domin tarwatsa  zanga-zangar mata da ke neman ‘yancin walwala a karkashin sabuwar gwamnatin da mayakan kungiyar ke shirin kafawa.

Wasu matan Afghanistan yayin zanga-zangar neman 'yanci a karkashin mulkin Taliban a cikin garin Kabul a ranar 3 ga Satumba, 2021.
Wasu matan Afghanistan yayin zanga-zangar neman 'yanci a karkashin mulkin Taliban a cikin garin Kabul a ranar 3 ga Satumba, 2021. AFP - HOSHANG HASHIMI
Talla

Zanga-zangar da matan suka yi ranar Asabar a birnin Kabul ita ce kashi na biyu da ke gudana a baya bayan nan a Afghanistan, tun bayan da Taliban ta karbe iko da kasar.

Gungun mata 50 ne suka fara tattakin na ranar Asabar zuwa fadar shugaban kasa, domin bayyana rashin amincewa da shirin Taliban na hana mata rike manyan mukaman sabuwar gwamnatin da suke shirin kafawa.

Tun lokacin da suka karbe mulkin kasar a ranar 15 ga watan Agusta, shugabannin Taliban sun yi alkawarin kare hakkokin mata a karkashin mulkinsu.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam da kasashen Turai na cike da shakku da alkawarin na Taliban, la’akari da cewar farko na mulkin kungiyar daga shekarar 1996 zuwa 2001 ba ta baiwa mata damar aikin yi ba, zuwa makaranta, ko kuma barin gidajensu ba tare ‘yan rakiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.