Isa ga babban shafi
Afghanistan

Sabon fada ya barke tsakanin Taliban da 'yan tawayen Panjshir

Rahotanni daga Afghanistan sun ce sabon fada ya barke tsakanin mayakan Taliban da na ‘yan tawayen da ke kiran kansu da NRF, a yankin kwarin Panjshir mai tsaunuka da ke arewa maso gabashin kasar.

Mayakan Taliban a Afghanistan.
Mayakan Taliban a Afghanistan. Aamir QURESHI AFP
Talla

Sabon gumurzun na zuwa ne a yayin da kungiyar Taliban ke shirin kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan bayan sake kwace iko da kasar a karo na biyu da ta yi.

Bayanai daga wasu majiyoyi sun ce da alama Taliban ta kuduri aniyar murkushe masu yi mata tawaye a yankin Panjshir ne kafin sanar da wanda zai jagoranci kasar bayan ficewar sojojin Amurka da na NATO, matakin da ya kawo karshen yakin shekaru ashirin da suka gwabza.

'Yan tawayen NRF masu adawa da kungiyar taliban a lardin Panshir na Afghanistan, 2 ga Satumba, 2021.
'Yan tawayen NRF masu adawa da kungiyar taliban a lardin Panshir na Afghanistan, 2 ga Satumba, 2021. AFP - AHMAD SAHEL ARMAN

Sai dai mayakan ‘yan tawayen na NRF da ke Panjshir, yankin da ya shafe kusan shekaru goma yana fafatawa da dakarun tsohuwar Tarayyar Soviet, da kuma mulkin farko na Taliban daga shekarar 1996 zuwa 2001, na cigaba da tsayuwar gwamen Jaki dangane da kin mika wuya ga Taliban.

Rundunar ‘yan tawayen na Panjshir ta kunshi mayakan sa kai masu adawa da kungiyar Taliban da tsoffin jami'an tsaron Afghanistan, wadanda suka ja daga a yankin mai tsunuka da ke da nisan kusan kilomita 80 da arewacin birnin Kabul, a karkashin jagorancin tsohon shugaban Amrulla Saleh da Ahmad Massoud, dan Ahmad Sha Massoud, tsohon kwamandan da ya jagoranci yaki da tarayyar Soviet da kuma adawa da zangon farko na mulkin Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.