Isa ga babban shafi
AMURKA-TALIBAN

Amurka ba zata sake mamayar wata kasa ba - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden yace lokacin tura sojojin kasar sa kasashen ketare domin mamaya ko kuma shiga gagarumin yaki domin dawo da su akan turba mai kyau ya kare.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden © CARLOS BARRIA, REUTERS
Talla

Yayin da yake jawabi ga al’ummar kasar dangane da dalilin da ya sa ya janye sojojin Amurka daga Afghanistan, abinda ya baiwa kungiyar Taliban damar karbe iko, Biden yace ba zai ci gaba da jefa rayuwar sojojin kasar sa cikin hadari ba.

Biden wanda ya dauki alhakin matakin da ya dauka, yace matakin shine mafi dacewa ga Amurka, duk da korafe korafen dake fitowa daga ciki da wajen Amurka dangane da janyewar.

Hotan sojan Amurka na karshe Janar Chris Donahue da ya fice daga Afghanistan
Hotan sojan Amurka na karshe Janar Chris Donahue da ya fice daga Afghanistan Jack Holt US Central Command (CENTCOM)/AFP

Shugaban yace daga wannan lokaci Amurka ba zata kwashi sojojin ta zuwa wata kasa da zummar mamaya ko kuma shiga yaki gadan-gadan, duk da yake kasar ba zata bada damar cutar da ita ko muradun ta daga wata kasa ba.

Biden yace duk wata kasar da ta cutar da Amurka ko kawayen ta zasu mayar da martani mai zafi, kuma duk wata kungiya ko mutanen da suka kai mata hari zasu zakulo su domin mayar da martanin da ya dace.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid
Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid REUTERS - STRINGER

Shugaban ya jinjinawa dakarun Amurka akan rawar da suka taka wajen kwashe mutane sama da dubu 120 cikin su harda wadanda suka fito daga kasashen kawayen su domin fitar da su daga kasar Afghanistan.

Bayan shekaru 20 da mamayar da Amurka ta yiwa Afghanistan, Biden yace sojojin Amurka sama da 2,400 suka mutu, yayin da ta kashe kudin da ya kai Dala triliyan 2 da miliyan dubu 300 wajen mamayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.