Isa ga babban shafi

Kungiyar Taliban ta gargadi Amurka da kawayenta

Kungiyar Taliban ta gargadi kasar Amurka da kawayenta a game da kara wa’adin ci gaba da kasancewar su a Aghanistan da sunan ci gaba da kwashe jama’ar su.Taliban din ta ce ba zata yiwa Amurka da kawayen tawani sassauci na ci gaba da zaman dakarun su a kasar matukar suka wuce mako mai zuwa ba.

Dakarun Amurka a filin tashi da na saukar jiragen Afghanistan
Dakarun Amurka a filin tashi da na saukar jiragen Afghanistan via REUTERS - US MARINES
Talla

Taliban din ta ce duk abinda ya samu jami’an Amurkako dakarun ta da suka wuce nan da mako daya a kasarda sunan kwashe jama’ar su to kuwa su kuka da kansu.

Ta ce babu wani dalili da zai sa ta yi maraba da kishin-kishin din kara wa’adin da Amurka da kawayen ta ke son yi na a kasar da nufin karkare kwashe mutanen su.

Tun da fari dai Amurka ta tsayar da ranar 31 da daya ga watan da muke ciki na Agusta a matsayin ranar da zata karkare kawashe jama’ar ta daga kasar, to sai dai dukannin Alamu na nuni da cewa hakan ba zai yiwu ba.

Mayakan taliban
Mayakan taliban AP - Rahmat Gul

Wannan ta sa tuni Burtaniya ta fara kira ga Amurkan data tsawaita wa’din don kwashe jama’ar cikin tsanaki, ba tare da sanyawa jama’a Fargabar za’a ta fi a bar su ba,

wanda hakan ke haifar da turmutustsun da ke sanadiyyar mutuwar mutane a filin jirgin saman Kabul.

Wasu daga cikin mayakan Taliban a birnin Kabul
Wasu daga cikin mayakan Taliban a birnin Kabul Hoshang Hashimi AFP

Taliban ta ce ta gama du wani shirin ta na kafa gwamnati mai cikakken Iko a don haka ko da soja daya ne ya rage da Amurka ko kasashe kawayen ta a kasar

ba zata kafa gwamnatin ba, kuma ba zata bar shi a haka ba zata dauki tsatsauran mataki a kansa.

Sai dai duk da wannan Barazana tuni dai Prime ministan Burtaniya Boris Johnson ya ce zai Burtaniya zata bukaci Amurka ta tsawaita wa’adin kwaso mutanen a yayin taron kasashe masu tattalin arziki na G7.

Daya daga cikin yankunan Panjshir, na Afghanistan
Daya daga cikin yankunan Panjshir, na Afghanistan Ahmad SAHEL ARMAN AFP

Sai dai har ya zuwa yanzu shugaban Amurka Joe Biden ko wata Hukuma ba ta ce komai dangane da batun kara wa’adin ko kuma mayar da martani kan barazanar Taliban din ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.