Isa ga babban shafi
SHARI'AR-ISLAMA

Ana fargabar Taliban zata dawo da shari'ar Islama a Afghanistan

Samun nasarar kwace iko da kungiyar Taliban tayi a kasar Afghanistan ya haifar da fargabar cewar tana iya komawa amfani da shari’ar Islama a cikin kasar.

Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid
Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid REUTERS - STRINGER
Talla

Kasashen Musulmi da dama a duniya na amfani da wani sashe na shari’ar Islama musamman abinda ya shafi dokokin dake da nasaba da harkokin iyali da zamantakewa, amma kuma kadan ne daga cikin su ke aiwatar da wasu hukunce hukuncen da shari’ar ta tanada da ake kira hudud.

Shari’a tdai sarin tafiyar da al’umma ne kamar yadda Qur’ani da Hadisan Mazan Allah Annabi Muhammad (SAW) suka tanada.

Sai dai ana samun rarrabuwar kawuna dangane da aiwatar da shari’ar tsakanin bangarorin addinin Islama da kuma kasashe.

Wasu daga cikin bangaren shari’ar da akafi amfani da su sosai sun hada da bangaren harkokin banki, abinda ya sa bankunan kasashen yammacin duniya ke aiwatar da tsarin Islama abinda ya janyo musu karuwar masu hulda da su daga cikin al’ummar Musulmi.

Tawagar jagororin Taliban
Tawagar jagororin Taliban AP - Rahmat Gul

Kalmar hudud na nufin iyaka da larabci, kuma bisa tsarin addinin Islama akan hukunta wadanda suka ketare iyaka wajen aikata laifuffuka irin su shan giya da fyade da luwadi da sata da kuma kisan kai.

Rahotanni sun ce kasashen Musulmi da dama basu cika aiwatar da manyan hukunce hukuncen da shari’ar Islama suka tanada ba saboda rashin samun shaidu kamar yadda doka ta tanada ko kuma amsa laifi daga wadanda ake zargi.

Daga cikin kasashen da ake aiwatar da sharia a duniya akwai Saudi Arabia wadda ke amfani da dokokin Islama wajen hukunta masu aikata laifuffuka ciki harda kisa ga wadanda suka aikata laifin kisan kai da bulala da kuma yanke gaba wanda aka saba yi a ranakun juma’a kafin Sallar Juma’a.

Ahmed Sani Yarima, tsohon Gwamnan Zamfara, kuma wanda ya fara aiwatar da shari'a Islama
Ahmed Sani Yarima, tsohon Gwamnan Zamfara, kuma wanda ya fara aiwatar da shari'a Islama © Daily Trust

Kasar Iran na daga cikin masu aiwatar da hukuncin Islama amma kuma alkalai na da damar amfani da shaidun da aka gabatar musu wajen yanke hukunci, abinda ya sa kasar ta zama daya daga cikin wadanda suka fi aiwatar da hukuncin kisa.

Kasar Brunei dake yankin Asia na daga cikin kasashen da suka aiwatar da shari‘ar Islama a shekarar 2019, abinda ya janyo mata suka daga kasashen duniya.

Wannan ya sa Sarkin Brunie yace ba zasu aiwatar da wasu tanade tanaden da suka hada da hukuncin kisa ta hanyar jifa da duwatsu ba.

Yankin Aceh dake kasar Indonesia na daga cikin masu amfani da shari’ar Islama a kasar dake dauke da Musulmi mafi yawa a duniya, inda ake yiwa masu laifi bulala a bainar jama’a saboda caca da shan giya da zina da kuma luwadi, sai dai gwamnatin kasar taki amincewa da aiwatar da hukuncin kisa.

Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiya tare da Franministan Qatar Sheikh Abdullah bin Nasser bin Khalifa Al Thani yayin wani taron kasashen yankin Gulf
Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiya tare da Franministan Qatar Sheikh Abdullah bin Nasser bin Khalifa Al Thani yayin wani taron kasashen yankin Gulf Reuters

Yankin Aceh na aiwatar da hukuncin kisa tun bayan da aka bashi yancin cin gashin kai a shekarar 2001.

Kasar Sudan ta fara amfani da shari’ar Islama a shekarar 1983, amma tun lokacin bata aiwatar da shi kamar yadda doka ta tanada.

Kasar bata aiwatar da hukuncin kisa duk da yake masu kare hakkin Bil adama na cewa ana yiwa daruruwan mata bulala kowacce shekara saboda aikata laifuffuka.

Shugaban mulkin sojin Pakistan Zia-ul-Haq ya gabatar da dokar shari’a a shekarar 1979, abinda ya baiwa kotuna damar aiwatar da dokokin sabanin wadanda turawan Birtaniya suka samar.

Batutuwan da kotun ke yanke hukunci akai sun hada da na kisan kai da zargi da sata da kuma shan giya ko kwayoyi, kafin sa hekarar 2006 da Yan majalisun kasar suka amince da dokar kare hakkokin mata, abinda ya sa aka dauke shari’ar fyade da kisan kai daga kotunan shari’a.

A Najeriya Jihohi 12 daga cikin 36 daga yankin arewacin kasar suka amince da dokar shari’a bayan dawowa Jamhuriya ta 4, abinda ya baiwa kotunan jihohin damar yanke hukuncin kisa da kuma yanke gabobi ga wadanda suka aikata laifuffukan da shari’a ta yiwa tanadi akai.

Sai kuma Qatar wadda ke amfani da bulala 100 wajen aiwatar da hukuncin zina, yayin da kuma ake yanke hukuncin kisa idan an samu mace Musulma da tayi zina da namijin da ba Musulmi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.