Isa ga babban shafi

Taliban ta bayyana yada za ta gudanar da mulkin Afghanistan

Kungiyar Taliban ta gudanar da taron manema labarai na farko, tun bayan kwace iko da ta yi da Afghanistan, inda ta yi shelar kawo karshen yakin da kasar ta shafe shekaru 20 a cikinsa, tare da sanar da yiwa dukkanin masu adawa da ita afuwa.

 Zabihullah Mujahid, mai magana da yahun yan Taliban
Zabihullah Mujahid, mai magana da yahun yan Taliban AP - Rahmat Gul
Talla

Yayin taron manema labaran, kakakin kungiyar ta Taliban Zabihulla Mujahid ya yi alkawarin baiwa mata damar gudanar da ayyuka bisa tsarin addinin Musulunci, sabanin yadda matan suka kasance a karkashin kungiyar a fiye da shekaru 20 da suka gabata.

Zabihullah Mujahid, mai magana da yahun yan Taliban
Zabihullah Mujahid, mai magana da yahun yan Taliban AP - Rahmat Gul

Mujahid ya kara da cewa nan gaba kadan za su kafa sabuwar gwamnati, sai dai bai yi cikakken bayan kan yadda za ta kasance ba, illa kawai za a baiwa dukkanin bangarori dama.

 

Jim kadan bayan, taron manema labaran na Taliban ne kuma mataimakin shugaban kungiyar Mullah Abdul Ghani Baradar wanda ya taka rawa wajen kafuwarta ya isa Kandahar, tsohon babban birnin Afghanistan a zangon farko na mulkin ‘yan Taliban fiye da shekaru 20 baya.

Taron manema labarai da yan kungiyar Taliban
Taron manema labarai da yan kungiyar Taliban Hoshang Hashimi AFP

Yayin tsokaci kan sauyin da aka samu a Afghanistan, jim kadan bayan taron gaggawa na ministocin waje na kasashen EU, babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turan Josep Borell ya ce dole su tattauna da kungiyar Taliban da a yanzu ke rike da madafun iko, la’akari da nasarar da suka samu, bayan rushewar gwamnatin da kasashen yamma ke marawa baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.