Isa ga babban shafi
Afghanistan

'Yan Taliban sun kusa kammala kifar da gwamnatin Afghanistan

Mayakan Taliban na gaf da cimma burin kwace iko da daukacin kasar Afganistan a yau Lahadi, bayan da a ranar Asabar suka mamaye wasu karin manyan birane, abinda ya sanya Kabul babban birnin kasar zama inda ya rage musu su murkushe.

Mayakan Taliban yayin sintiri a titunan birnin Herat da suka kwace. 14 ga Agusta, 2021.
Mayakan Taliban yayin sintiri a titunan birnin Herat da suka kwace. 14 ga Agusta, 2021. REUTERS - STRINGER
Talla

A jiya ne dai kungiyar ta Taliban ta kwace iko da Jalalabad, babban birnin yankin gabashin Afghanistan, sa'o'i kadan bayan mamaye garin Mazar-i-Sharif birni na hudu mafi girma dake areacin kasar, nasarorin bazatar da suka samu cikin kwanaki 10.

Wani zaunin birnin na Jalalabad Ahmad Wali ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa sun wayi gari da ganin fararen tutocin Taliban a fadin birnin, zalika sun kwace iko ne ba tare da fafatawa da sojojin gwamnati ba, kamar yadda itama kungiyar ta Taliban ta sanar.

Tuni dai Shugaba Joe Biden ya ba da umurnin tura karin sojojin Amurka zuwa Afghanistan don tabbatar da kwashe Amurkawa da kuma wasu dubban ‘yan kasar cikin gaggawa daga ofishin jakandancin Amurkan da ke birnin Kabul, don kaucewa ramuwar gayya daga mayakan Taliban, kan mutanen da suka kwashe shekaru suna aikin taimakawa dakarun Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.