Isa ga babban shafi
Afghanistan

Shugaban Afghanistan ya sha alwashin dakatar da zubar da jini a kasarsa

Shugaban Afghanistan da ke cikin mawuyacin hali ya sha alwashin kawo karshen zubar da jini a kasar, a daidai lokacin da mayakan Taliban ke kara kusantar cimma burinsu na kwace iko da birnin Kabul.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani.
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Cikin jawabin nasa shugaban na Afghanistan ya ce dakatar da tashin hankalin da kasar ke ciki shi ne babban burinsa na tarihi a halin yanzu.

Jawabin shugaba Ghani da aka nada shi ne na farko da ya gabatarwa al’ummar kasar, tun bayan da Taliban ta kaddamar da farmaki kan dakarun gwamnati tsawon kusan makwanni 2.

Mayakan Taliban bayan kwace iko da birnin Herat.
Mayakan Taliban bayan kwace iko da birnin Herat. - AFP

Ashraf Ghani dai bai nuna alamar cewa zai yi murabus ko kuma daukar alhakin rugujewar rundunar sojin Afghanistan, illa sanarwar da yayi kan cewa yanzu haka yana tattaunawa da shugabancin Taliban domin kawo karshen yaki, gami shirin farfado da karsashin dakarun kasar.

Jawabin na Ghani ya zo ne bayan da Amurka ta aike da sojojinta don kwashe ma’aikatan ofishin jakadancinta da kuma dubban ‘yan Afghanistan da iyalansu, wadanda ke fargabar fuskantar mayakan Taliban ka iya hukunta su saboda yi wa Amurka aiki a cikin shekaru 20 na mamayar da ta yiwa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.