Isa ga babban shafi
RIKICIN-AFGHANISTAN

Mayakan Taliban sun kama hanyar zuwa birnin Kabul

Mayakan kungiyar Taliban sun sake kwace karin garuruwa a ci gaba da nasarar da suke samu na kokarin karbe iko da kasar Afghanistan yayin da Amurka da Birtaniya ke kan hanyar kai dubban sojoji domin kwashe Yan kasashen su da suka makale a birnin Kabul.

Mayakan Taliban a birnin Herat na 3 mafi girma a Afghanistan
Mayakan Taliban a birnin Herat na 3 mafi girma a Afghanistan - AFP
Talla

Umurnin kwashe Yan kasashen wajen ya biyo bayan kwace iko da Kandahar da Taliban tayi wanda shine birni na biyu mafi girma, yayin da mayakan suka nufi birnin Kabul, babban birni guda da ya rage bai fada hannun su ba.

Gaggauta kwace garuruwa da kungiyar Taliban keyi ya baiwa jama’ar kasar da kungiyar kawancen Amurka wadda ta kashe biliyoyin daloli wajen kifar da gwamnatin Taliban bayan harin 11 ga watan Satumbar da aka kai Amurka kusan shekaru 20 da suka gabata mamaki.

Jami’an tsaron Afghanistan sun gaza kare garuruwan dake cikin kasar, inda rundinoni da dama suka mika kai ga mayakan Taliban cikin ruwan sanyi ba tare da wani fafatawa ba.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson da Sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg sun bayyana goyan baya ga gwamnatin Afghanistan
Firaministan Birtaniya Boris Johnson da Sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg sun bayyana goyan baya ga gwamnatin Afghanistan KENZO TRIBOUILLARD POOL/AFP

Babban birnin Yankin Loghar Pul-e-Alam shine mafi girma da ya fada hannun mayakan yau juma’a, abinda ya rage kilomita 50 tsakanin mayakan da birnin Kabul mai dauke da fadar gwamnati.

Birtaniya ta zargi tsohon shugaban Amurka Donald Trump da tattaunawa da kungiyar Taliban, matakin da ya bada kofar janye dakarun kasar, abinda ya basu damar kaddamar da munanan hare hare.

Firaminista Boris Johnson yace ba zasu juyawa mutanen Afghanistan baya ba, duk da janyewar jami’an ofishin Jakadancin kasar.

Mayakan Taliban a Kandahar
Mayakan Taliban a Kandahar - AFP

Johnson yace zasu ci gaba da goyawa halartaciyar gwamnatin Afghanistan baya jim kadan bayan gudanar da wani taron manyan jami’an sa dangane da abinda ke faruwa a cikin kasar.

Ita ma kungiyar NATO bayan wani taron gaggawa da ta kira yau juma’a tace zata ci gaba da baiwa sojojin Afghanistan taimakon da ya dace.

Sakataren ta Jens Stoltenberg yace burin su shine taimakawa sojoji da sauran jami’an tsaron kasar domin kare jama’ar kasar, yayin da yace zasu ci gaba da barin ofishin jakadancin su a bude a Kabul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.