Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Mayakan Taliban sun yi wa fararen isgilanci

Mayakan Taliban na ta kyalkyalewa da dariya a daidai lokacin da fareren hula ke ficewa daga birnin Kunduz da mayakan suka karbe bayan sun fatattaki sojoji.

Wasu daga cikin mayakan Taliban a Afghanistan
Wasu daga cikin mayakan Taliban a Afghanistan AP - Mohammad Asif Khan
Talla

Daya daga cikin mayakan mai duddusan gemu da ke sintiri a birnin, ga kuma bindiga rataye a kafarsa, na ta kecewa da dariya har kunne a daidai lokacin da yake miko saraka ga jama’a daga tagar motarsa.

Mayakan da ke cike da farin cikin ficewar sojojin Amurka daga Afghanistan, sun mamaye unguwanni birnin na Kunduz da kuma wasu manyan lardunan kasar bayan sun kwace su a hare-haren da suka kaddamar a karshen mako.

Kimanin garuruwa tara ne suka fada hannun mayakan a makon jiya, amma a wannan Larabar ce suka kwace Kunduz baki dayansa bayan sun fatattaki daruruwan sojojin Afghanistan.

Yanzu haka wadannan mayaka sanye da kakin soji na ta kara-kaina a birnin a kan babura da kuma motocin da suka kwace daga hannun sojoji.

Kazalika saboda samun wuri, mayakan na Taliban na ta yin kwambo domin daukar hotuna saboda murnar nasarar da suka samu.

A shekarun 2015 da 2016, Taliban ta taba kwace birnin na Kunduz kafin daga bisani sojojin Afghanistan suka sake karbewa tare da taimakon dakarun Amurka a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.